Shalkwatar rundunar ‘yansanda ta kasa ta tabbatar da kama wasu jami’an yansanda guda ukku da aka gani cikin wani faifan bidiyo suna yin harbi cikin iska a lokacin da suke tare da fitaccen mawakin siyasar nan,Dauda Adamu Kahutu, wanda aka fi sani da Rarara.
Jami’an yansandan sun hada da Sergent Abdullahi Badamasi da Segernt Isah Danladi da kuma Insifekta Dahiru Shu’aibu, wadanda sune ke tsaron lafiyar fitaccen mawakin.
An samu jami’an ‘yansandan suna harbi da bindiga kirar Pistol da kuma kirar Ak 47 a lokacin da suke raka mawaki Rarara domin ya shiga cikin motarsa a wajen wani rabon kayan abinci da ya yi a mahaifarsa.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar yansanda ta kasa, CSP Olumiyiwa Adejobi shine ya tabbatar da kama jami’an yansandan a shafinsa na twitter, Ya ce a yanzu haka suna hannunsu, kuma yayi alkawarin yin cikakken jawabi da zarar an kammala gudanar da binciken da za’a yi masu.