Mataimakin sufeton ‘yansandan kasar nan mai kula da shiyya ta daya dake nan Kano, Sani Bello Dalijan, Ya ce Jami’an ‘yansanda sun yin amfani da dabaru daban daban domin dakile duk wata barazana ta tsaro da aka fuskanta a zaben shugaban kasa da aka yi.
Dalijan ya baiyana haka ne a yayin ganawarsa da manema Labarai da yammacin jiya a Ofishinsa.
Sai dai kuma ya ja kunnen daukacin jami’an yansanda da zasu yi aikin tabbatar da tsaro a zabe mai zuwa dasu kasance ‘yan baruwana da shiga harkokin siyasa.
Mataimakin sufeton ‘yansanda mai kula da shiyya ta daya,Ya ce an tanadi isassun kayan aiki na dakile duk wata barazana ta rashin tsaro, sannan kuma ya yi kira da a tabbatar anyi zaben cikin kwanciyar hankali da lumana.
Wakilinmu Bashir Faruk Durumin Iya ya ruwaito mataimakin sufeton yansandan na kasa mai kula da shiyya ta daya, Na jan hankalin iyaye da shugabannin addinai dasu yi kira ga mabiyansu da kuma matasa wajen kauracewa daukar makami ko kuma shiga bangar siyasa a lokacin zabe.