Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce ba a samu asarar rai ba sakamakon gobarar da ta afku da yammacin ranar Asabar a shalkwatar rundunar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar Abdullahi Haruna-Kiyawa, ya tabbatar da faruwar al’amarin a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a karshen mako.
A cewar sanarwar, ofisoshin da gobarar ta kone sun hada da offishin jami’n gudanarwa da mulkin da Offishin hulda da jama’a da offisoshin kula da harkokin kudi da dai sauransu.
Amma babu abunda ya samu bayanan rundunar.
Sanarwar tace mataimakin gwamnan jihar Kano, Nasiru Gawuna, ya ziyarci shalkwatar da al’amarin ya faru, domin jajantawa rundunar ‘yan sandan.
A madadin gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, Gawunaya jajantawa babban sufeton 'yan sanda na kasa Usman Alkali Baba kan gobarar da ta kone ofisoshi da dama a shalkwatar ‘yan sandan.
Nasiru Gawuna, ya ziyarci shalkwatar ‘yan sandan da ke yankin Bompai domin duba irin barnar da gobarar ta haddasa.