Rundunar ‘yan sandan jihar Filato ta tabbatar da cewa jami’anta sun kama dan takarar gwamna na jam’iyyar Labour a jihar, Yohanna Margif.
Da yammacin ranar Alhamis ne jami’an tsaro suka yi awan gaba da Margif bulaguro bayan da ake ta cece-kuce akan ya ajiye mukaminsa na takarar gwamna a jam’iyyar Labour, zargin da ya musanta.
Da yake tabbatar da kama dan takarar a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Alabo Alfred, ya bayyana cewa sabanin rahoton da ake yadawa kama Margif ba shi da alaka da siyasa.
Alabo ya ci gaba da cewa wani abokin kasuwancinsa, E.C. Gajare shine ya kai karar dan takarar, inda ya yi zargin cewa Margif ya ba shi cakin bankin na bogi kan wata huldar kasuwanci da suka yi a kwanakin baya.