Kwamishinan ‘yan sandan jihar Rivers, Okon Effiong, ya ce sun saki lauyoyin jam’iyyar APC a jihar da aka kama bayan an tabbatar da cewa takardun da aka gansu da su ba na bogi ba ne.
Da yake magana a gidan Talabijin na Channels, kwamishinan ‘yan sandan ya ce a ranar Asabar, wasu masu bada rahoto a wani otal suka sanar da cewa wasu baki suna buga takardu na bogi dake kama sakamakon zabe na hukumar INEC.
Da yake amsa tambayoyyi, Effiong ya ce ‘yan sanda sun tunkari kotu domin samun izinin bincike wanda aka aiwatar da shi da safe.
Kwamishinan ‘yan sandan na jihar Rivers, ya ce a lokacin da suka isa otal din, ‘yan sanda sun ga mutane takwas a cikin dakuna uku tare da kwamfutar tafi-da-gidanka da wasu takardu.
Ya kara da cewa uku daga cikin lauyoyin an sake su ne bayan sun gane cewa su lauyoyi ne yayin da wasu biyar kuma aka sake su ga wadanda suka tsaya musu.