Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa za ta gurfanar da wani direban kwale-kwale mai suna Aminu Musa a gaban kotu bisa laifin yin lodin wuce kima da kuma tuki a cikin dare biyo bayan mutuwar fasinjoji 2 tare da ceto mutum 4 yayin da mutum 1 ya yi batan dabo a karamar hukumar Auyo dake Jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Lawal Shisu Adam wanda ya bayyana haka ta cikin wata sanarwa, ya ce an kama Musa mai shekara 39 dan karamar hukumar Kaugama a ranar Lahadi kuma halin yanzu yana hannun ‘yan sanda.
Ya kara da cewa direban ya tabbatar da cewa ya dauki mutane 7 da babur guda daya da suka hadar da shi kansa da direban sa mai suna Isa Wailare yayin da kwale-kwalen ya kife a sakamakon kadawar Igiyar ruwa.
Shisu ya ce yayinda ake cigaba da laluben direban kwale-kwalen na biyu a cikin ruwa, za a gurfanar da Aminu a gaban kotu bisa laifin yin lodin fiye da kima da tuki a cikin dare.