Rundunar sojojin Najeriya ta kori wasu dakarunta biyu bisa kisan wani malamin addinin Islama, Sheikh Goni Aisami Gashua, a jihar Yobe.
Sojojin da aka kora sun hada da Kofur John Gabriel da Kofur Adamu Gideon.
Gidan talabijin na channels ya rawaito mukaddashin kwamanda mai kula da bataliya ta 241 dake guru a jihar Yobe, Laftanar Kanar Ibrahim Osabo, ya shaidawa manema labarai cewa, kwamitin binciken hadin gwiwa da aka kafa tare da hadin gwiwar ‘yan sanda ya same su da laifi.
Ya ce an sallami sojojin biyu ne bisa tuhume-tuhume biyu.
Osabo ya kara da cewa za a mika sojojin da aka kora a hannun ‘yan sanda a Damaturu domin gurfanar da su a gaban kotu.
A karshen makon jiya ne aka samu labarin kashe Sheikh Goni Aisami-Gashua.
Wasu mazauna Gashua sun ce lamarin ya faru ne da karfe 10 na safe a yankin Jajimaji mai tazarar kasa da kilomita 30 daga Gashua, mahaifar shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan.
Wadannan mutane da ‘yan sanda suka gabatar da su a ranar 23 ga watan Agusta, 2022, ana zargin suna da hannu a kisan malamin a jihar Yobe.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Dungus Abdulkarim, a wata tattaunawa da manema labarai ta wayar tarho, ya ce an kama wadanda ake zargin dauke da bindigogi kirar AK-47 kuma suna hannun ‘yan sanda.
Tuni shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da kisan.”