On Air Now

ZANGON RANAR ASABAR

Noon - 6:00pm

Rundunar Sojojin Sama A Najeriya Ta Kubutar Da 'Yan Kasar Sin 7 Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane

Gwamnatin jihar Neja ta sanar da kubutar da wasu ‘yan kasar Sin 7 da ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da su a wani hari da suka kai a wani wurin hakar ma’adinai da ke Ajata zuwa Aboki a karamar hukumar Shiroro ta jihar bayan kimanin watanni shida.

An yi garkuwa da Sinawan a ranar 29 ga watan Yuni na  2022 lokacin da daruruwan mahara cikin ayari  suka kai hari a wurin hakar ma'adinan inda aka kashe sojoji da 'yan sandan kwantar da tarzoma.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida a jihar, Emmanuel Umar, wanda ya tabbatar  da hakan a wata sanarwa da ya fitar a Minna, babban birnin jihar, ya ce rundunar sojojin sama ta ce ta gudanar da  aikin ceto mutanen.

Ya kara da cewa  an kubutar da ‘yan kasar ta Sin ne a wani yanki na karamar hukumar BirninGwari ta jihar Kaduna.