Babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, a ranar Talata, ya halarci jana’izar mutanen da suka mutu, inda ya bayyana mummunan harin da aka kai ta sama wanda ya kashe akalla mutane 85 a matsayin abin takaici.
Babban hafsan sojojin wanda ya ziyarci wurin da al'amarin ya faru, ya nemi afuwa a madadin rundunar sojin Najeriya ga al’umma da gwamnati, da kuma al’ummar jihar Kaduna.
Lagbaja ya yi alkawarin kiyayewa daga faruwar irin wannan abu wajen gudanar da ayyukan soji.
Haka kuma Shugaban Rundunar Sojojin Najeriya Janar Christopher Musa da Lagbaja sun ziyarci wadanda suka jikkata a asibitocin Kaduna a ranar Talata.