Shalkwatar rundunar hadin gwiwa ta shiyyar ta 2 a Arewa maso Gabas dake gudanar da shirin simame na Operation Hadin Kai, ta fara gudanar da bincike domin gano sojojin da ake zargi sun kashe wani malamin addinin Islama a jihar Yobe.
Mataimakin daraktan hulda da jama’a na rundunar Cpt. Kennedy Anyawu, ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Damaturu.
Rundunar ‘yan sanda dai ta kama wasu sojoji biyu bisa laifin kashe wani malamin addinin Islama, Sheikh Goni Aisami Gashua a ranar Juma’a.
Anyawu ya bayyana al’amarin a matsayin abin takaici matuka ganin yadda Sashen ba ya lamuntar karya ka’idar aiki ga dakarun soji.