
A karo na biyu, Rundunar sojin kasar nan ta yi gargadin shirya kowace irin makarkashiya domin kawo tazgaro wajen mika mulki ga zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu, a ranar 29 ga watan da muke ciki.
Daraktan yada labarai na shalkwatar tsaro ta kasa, Manjo Janar Musa Danmadami,shi ne ya yi gargadin, Wata daya ke nan bayan da daraktan yada labarai na rundunar soji ta kasa, Birgediya janar Tukur Gusau ya ci alwashin cewar rundunar zata dakile duk wani yunkuri na kawo tazgaro ga tsarin dimukuradiyyar kasa.
Wasu daga cikin ‘Yan takara da suka harzuka sun kalubalanci rantsar da zababben shugaban kasar tare da yin kira da a kafa gwamnatin rikon kwarya a Najeriya.
Sai dai da yake yiwa manema Labarai jawabi a shalkwatar tsaro ta kasa dake Abuja, Janar Danmadami, ya ce sojoji sun shirya tsaf domin tabbatar da cewar babu wata kitimurmura da aka kulla domin kawo nakasu ga mika mulkin.