Rundunar sojin kasar nan ta amince da Sallamar wani kurtun soja tare da wasu dakarun soji 242 dake bangarori daban daban na kasar nan.
Ana saran sojojin da abun ya shafa zasu fara hutun dole daga ranar 15 ga watan janairun 2023, yayin da za’a kammala sallamar su daga bakin aiki a ranar 15 ga watan fabarairun 2023.
Rahotanni sun baiyana cewa mafi yawa daga cikin sojojin da abun ya shafa sun ajiye aikin ne sakamakon matsalolin da suka shafi rashin lafiya, a yayin da kuma wasu bisa radin kansu suka ajiye aikin.
Wata takarda data fita a ranar 15 ga watan da muke ciki, Ta baiyana cewa an umarci sojojin da abun ya shafa su rubuta takardar barin aiki a ranar 15 ga watan Oktoban bana, sannan kuma su mika dukkanin Kakakinsu da sauran bindigogi da harsashin dake wajensu.
Mai magana da yawun rundunar soji ta kasa, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya tabbatar da sallamar sojojin daga bakin aiki kamar yadda babban hafsan sojin kasa ya amince da yin hakan.