Rundunar soji na kasa ta sake musanta zargin cewar jami’anta na shirin Gudanar da zanga-zanga asakamakon tabarbarewar yanayin aiki da kuma Rashin biyansu hakkokinsu .
Koda a Ranar 18 ga watan Mayun Bana, Rundunar ta sake karyata irin wannan ikirari.
Kazalika cikin wata sanarwa da Daraktan yada labaran Rundunar, Birgediya janar Onyema Nwanchukwu ya fitar ya baiyana ikirarin amatsayin wanda babu kanshin Gaskiya acikinsa wanda kawai aka kirkira domin batawa rundunar suna
Ya kuma zargi duk wadanda suke ikirarin da kokarin haifar da Rudani atsakanin jami’anta
Bugu da kari, Onyema ya kara da cewa awani banagare na inganta ayyukan jami’an, Rundunar ta samar da wani tallafi karkashin shugabancin RUNDUNAR SOJI TA KASA domin inganta walwalar dakarun