On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Rukunin Kamfanin BUA Yace Ba Ya Bukatar Filin Gwamnatin Jihar Kogi Kadada Dubu 50

Rukunin kamfanin BUA yace yanzu ba ya sha’awar mallakar fili mai fadin kdadada dubu 50 da ya samu daga gwamnatin Kogi a shekarar 2012.

Kamfanin ya bayyana hakan ne a wata wasika da ya aikewa babban daraktan ofishin filaye da raya birane na jihar ta Kogi.

Majalisar dokokin Kogi dai ta gayyaci kamfanin BUA domin bayyana dalilin da ya sa ya ki biyan kudin filin da kuma dalilin da ya sa ya ki biyan diyya ga al’ummar da abin ya shafa.

Sai dai a cikin wasikar kamfanin yace dama bai mallaki filin ba.

Kamfanin ya yi ikirarin cewa ba zai iya amfani da filin ba saboda rashin abubuwan da ake bukata da kuma kalubalen tsaro a jihar.

Wasikar tace tun bayan da Kamfanin ya amsa gayyatar zuba jari a Jihar Kogi a shekarar 2012, babu wani yunkuri da gwamnatin jihar tayi wajen samar da hanya ko kayan more rayuwar da zai karfafa masa amfani da filin kamar yadda suke bukata.

BUA yace yanzu haka babu hanyar zuwa filin da ake magana akai sai ta cikin ruwa, kuma matsalar tsaro a wurin ta sa ba zasu iya zuba jarinsa a filin ba kamar yadda suke bukata.

Kamfanin yace binciken masana da suka yi a filin ya nuna musu cewar kashi 30 ne kawai na filin ke da inganci, yayin da kashi 66 duk duwatsu ne da tsaunuka wadanda ba zasu basu damar gudanar da aikin da suke bukata ba.

Saboda wadannan dalilai Kamfanin BUA ya shaidawa gwamnatin jihar Kogi cewar baya bukatar filin kuma sun dakatar da shirin zuba jarin da suke da shi a wurin.

Kamfanin yace da filin ya cika muradunsu da tuni sun biya shi kafin fara duk wani aiki kamar yadda manufofinsa yake a ko ina, saboda haka gwamnatin jihar Kogi na da hurumin soke takardar mallakar filin ba tare da wani haufi ba.