Jirgin dauke da maniyata 472 daga jihar Nassarawa da jami'ai 27 ya sauka a filin jirgin saman Muhammad Ibn Abdu-Azeez dake Madina da karfe 3:20 na dare.
Jakadan Najeriya a kasar Saudiyya, Ambasada Yahaya Lawal tare da karamin jakadan Madina, da tawagarsa sun kasance a filin jirgin saman domin tarbarsu.
A bisa al'ada ma'aikatar aikin hajji da umrah ta kasar Saudiyya da jami'an ofishin jakadancin Najeriya a kasar sun yi shiryawa maniyyatan liyafar tarba a filin jirgin saman.
Suwaiba Ahmed dake sashen yada Labarai da wallafa bayanai a hukumar NAHCON ta rawaito a jawabinsa na maraba, Ambasada Yahya Lawal ya godewa Allah da ya sauki matafiyan lafiya, ya kuma bukace su da su kasance jakadu nagari ga Nijeriya a kowane lokaci.
Ya kuma yi kira gare su da su yi addu’a don cigaba da hadin kan Nijeriya.
Daga karshe kuma a yi musu addu'ar yin ibadar Hajji karbabbiya.
Daga nan aka kai maniyyatan masaukinsu.