Tawagar farko ta jami’ai 31 na Hukumar kula da aikin hajji ta kasa NAHCON, sun tashi zuwa kasar Saudiyya daga filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, gabanin fara jigilar maniyatan 2023.
A wata sanarwa dauke da sahannun mataimakin daraktan yada labarai na hukumar Mousa Ubandawaki, tawagar da ta kunshi jami’ai 21 da ma’aikatan lafiya 10, wadanda za su je kasar Saudiyya domin shirye-shiryen karshe na karbar sahun farko na maniyyatan Najeriya.
A wani takaitaccen taro na bankwana da aka gudanar gabanin tashinsu zuwa kasa mai tsarki, Shugaban Hukumar NAHCON, Zikrullah Kunle Hassan, ya bayyana aikin Hajji amatsayin abin da ya shafi duniya baki daya, wanda ke da nufin samar da hadin kai a tsakanin Musulmi da sauke farali.
Ya umurci jami’an da su dauki aikinsu da muhimmanci ta hanyar zakulo hanyoyin da suka dace don samun nasara a aikinsu.
Shima da yake jawabi a wajen taron, kwamishinan tsare-tsare da da ma’aikata, gudanarwa da kudi, Alhaji Nura Hassan Yakasai, ya bada tabbacin hukumar NAHCON na bada goyon baya da karfafa ayyukan Jami’an.
A ranar Alhamis 25 ga watan Mayu ne aka shirya fara jigilar maniyyatan aikin hajjin bana daga Najeriya zuwa Saudiyya, inda jihar Nasarawa za ta fara jigilar maniyyatanta.