On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Rudani Kan Ganin Hoton Sunusi Na II A Gidan Gwamnatin Kano

Gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf, ya ce babu wani shiri na tube rwanin mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Bayero tare da mayar da Malam Muhammadu Sunusi na II.

 

Gwamnan ya mayar da martani ne a kan wani hoto da aka  gani na Muhammadu Sanusi na II dakin taro da ke gidan gwamnati wanda ya haifar da rudani da cece-kuce  cewa ana shirin  dawo da Sanusi.

Mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya fayyace cewa tarihin zauren nadin sarautar ya yi daidai da Muhammadu Sanusi na II, shi ya sa aka sanya hotonsa a dakin taron.

A cewarsa, an gina zauren ne domin gabatar da sandar mulki ga Mallam Muhammadu Sanusi na II jim kadan bayan da aka nada shi sarauta a shekarar 2014, inda ya ce dawo da hotonsa wani bangare ne na gyaran da ake yi domin baiwa zauren kulawa da daukar sabon yanayi.