Mataimakin shugaban jam’iyyar Labour a yankin kuduncin kasarnan, Lamidi Apapa, da wasu mambobin kwamitin gudanarwa na jam’iyyar na kasa sun ce sun karbi ragamar tafiyar da harkokin jam’iyyar.
Hakan ya biyo bayan hukuncin da kotu ta yanke na hana Julius Abure da wasu mutane uku bayyana kansu a matsayin jami’an jam’iyyar na kasa.
Wannan ta faru ne a Abuja ranar Alhamis yayin wani taron gaggawa na kwamitin gudanarwa na jam’iyyar ta Labour na kasa.
Lamidi ya ce a yanzu shi ne shugaban riko na jam’iyyar na kasa yayin da Saleh Lawan yake rike da mukamin sakataren riko na kasa.
Julius Abure ya dage cewa har yanzu shine shugaban jam’iyyar Labour na kasa, tare da samun goyon bayan kungiyar kwadago ta Najeya NLC.
Aburere ya yi watsi da abin da ya bayyana amatsayin haramtattun ‘yan majalisar zartarwa na jam’iyyar bisa jagorancin Lamidi da Salehan sun yi alkawarin karbar ragamar tafiyar da harkokin jam’iyyar.
Abure ya caccaki matakin kuma ya zargi ‘yan sanda da hada kai da su domin shiga sakatariyar jam’iyyar da ke Abuja.
Ya zargi jam’iyyar APC mai mulki da hannu a wannan makarkashiya, ya kuma yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya ja hankulan jam’iyyarsa.