Shugaban Kungiyar Malaman Jami’oi ta kasa ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke, Yace Da ace Yaran Yan siyasar kasar nan na zuwa Makarantun gwamnati da tun farko an magance yajin aikin da kungiyar ta kwashe watanni biyar tana kan yi.
A ranar Talata ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ya bawa Minsitan Ilimi Adamu Adamu, Wa’adin Makwanni Biyu, Da ya tabbatar an kawo karshen yajin aikin da kungiyar ta ASUU ke yi.
Da yake mayar ta martani akan wa’adin da Shugaban kasar ya bayar, Shugaban Kungiyar ASUU, Yace lokacin da shugaban kasar ya bayar yayi tsawo da yawa, sannan kuma kungiyarsu zata iya janye yajin aikinta a cikin kasa da kwana biyu, idan har gwamnatin taraiyya zata mutunta yarjejeniyar da suka kulla.
A yayin wani taron manema Labarai da kungiyar ta ASUU ta kirawo a ranar Talata, Farfesa Osodeke, Ya zargi Ministan kwadago, Chiris Ngige da yin zagon kasa.
Daga cikin bukatun da kungiyar ASUU tasa a gaba sun hada da, Samar da Kudaden Farfado da Jami’o, da Kudadensu na Alawus da kuma manhajar da za’a rika yin amfani da ita wajen biyansu albashi.