Kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta kasa IPMAN, tace layukan man fetur da suka sake kunno kai a wasu sassan babban birnin tarayya Abuja, hakan ya biyo bayan karancin man fetur daga kamfanin mai na kasa.
Mataimakin shugaban kungiyar IPMAN na kasa, Abubakar Maigandi ya bayyana hakan a ranar Talata yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja.
Maigandi ya bayyana cewa, saboda rashin samun man fetru daga NNPC, hakan ya sa man ya yi karanci a depo-depo masu zaman kansu inda ‘yan kasuwa ke lodi.
Ya kara da cewa karancin da aka samu a baya-bayan nan ya kuma haifar da tashin farashin man daga Naira 148 zuwa tsakanin Naira 170 zuwa Naira 175 a gidajen mai.
Har yanzu dai kamfanin NNPC da sashen albarkatun Man Fetur ba su fitar da wata sanarwa ba game da halin da ake ciki a baya-bayan nan.