Karamin Ministan Aiyuka, Umar Ibrahim, Yace Biyan diyya itace Babban abunda yake kawo tarnaki wajen gudanar da aikin titin Kano zuwa Gwarzo dake nan jihar Kano.
Ministan ya baiyaan haka ne a ranar Lahadi, yayin ziyarar gani da ido da ya kawo nan jihar Kano domin ganin yadda aikin ke gudana.
El Yakubu, Yace hanyar Kano zuwa Gwarzo ta karasa garin Dayi dake jihar Katsina wadda tsawonta ya kai kilomita 90 da digo 65 , wadda ta hada jihar Kano da wasu jihohi na yankin arewa maso yammacin kasar nan, da kuma wasu jihohi na Arewa ta tsakiya ta fara ne tun daga kan gadar sama data kasa ake Kabuga a nan jihar kano.
Karamin Minsitan Aiyuka.
Bugu da kari karamin ministan yace an fuskanci wasu daga cikin matsalolin ne bayan an fara kason farko na aikin wanda zai bi ta wasu daga cikin garuruwan Doka, Rimini Gado Sai Garo da Gwarzo da kuma Garin Dayi dake jihar Katsina, wanda dukkaninsu suna bukatar a biyasu diyya.