On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Rarara Zai Cigaba Da Biyan Albashi Ga 'Yan Sandan Najeriya Dake Tsaron Lafiyarsa Bayan Korarsu Daga Aiki

Fitaccen mawakin siyasa Dauda Adamu Abdullahi Kahutu wanda akafisani da Rarara y ace zai dauki nauyin cigaba da biyan albashin Jamian ‘yan sandan nan guda uku da suke bashi kariya, wanda rundunar ‘yan sandan Najeriya  koresu daga bakin aikin sakamakon rashin mutunta dokokin aiki.

Idan za’a iya tunawa, Rundunar ‘yan sanda ta kasa ta kori wasu ‘yan Sanda guda uku wanda suke bada  rakiya ga mawaki Rarara, saboda harba bindiga da sukai ba bisa ƙa’ida ba, lokacin da suka raka Rarara mahaifarsa ta Kahutu a jihar Katsina,Inda yayi rabon kayan abinci.

A wata tattaunawa da manema labarai a Kano, Rarara wanda shi ne shugaban kungiyar 13+13 yace bayan sallamar ‘yan sandan daga aiki sun sanar da shi, kuma  ya tambaye su adadin abun da ake biyansu, matsayin albashi kuma nan take yayi alkawarin cigaba da biyansu, har lokacin da za’a amsa rokon da suka daukaka.

Haka kuma ya sanya bidiyon wasu jami’an ‘yan sanda suna harba bindigu sama, Inda ya roki rundunar da kada ta kore su saboda laifin da sukai yayi dai-dai da irin abun masu tsaronsa suka yi.

” Sun fadamin cewa sun  shigar da roko kuma na ce su cigaba da neman hakkinsu, Amma dai na gaya musu idan babana ya zo , to babu shakka za’a Mayar da su bakin aikin su, kuma kowa yasan Baba nan zai zo mulkin Najeriya nan bada jimawa ba”. Acewar  Rarara

Cikin wasu kalamai na ganin baiken korar ‘yan sandan, Mawakin siyasar ya kara da cewa ” An kona min gida, an kona ofishina an kuma kona min plaza, Kuma an san akwai masu neman illata ni ko ma rayuwa ta baki daya, amma duk da haka aka dauki wannan matakin akan masu bani tsaro, to ba komai nan bada jimawa ba baban zai zo, duk da na nemi alfarma amma aki ayi min”.