Yayinda hankula suka karkata ake dakon hukuncin kotun koli kan shari'ar zaben gwamnan Jihar Kano Dauda Adamu Kahutu Rarara, fitaccen mawakin siyasa na jam’iyyar APC, ya bayyana bukatar samun zaman lafiya a tsakanin al'umma.
Da yake zantawa da manema labarai kan muhimmancin tallafawa hukumomin tsaro, musamman ‘yan sandan Najeriya, wajen wanzar da zaman lafiya a jihar Kano ya jaddada bin alfanun biyayya ga doka da oda, uana mai kira a inganta zaman lafiya, inda ya bukaci mazauna Kano da su bayar da tasu gudunmawar wajen samar da zaman lafiya kan duk wani abu da ya shafi hukuncin kotun.
Rarara ya tunatar da al’ummar Kano yadda aka bijirewa oda da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta sanar da wanda ta lashe zaben gwamna da ya gabata na 2023.
Ya ce gwamnatin APC a lokacin ta bi doka, inda ta mika mulki ga dan takarar jam’iyyar NNPP. Daga baya kuma, APC ta bi matakan da doka ta bada dama, inda ta kalubalanci nasarar da NNPP ta samu a kotun sauraron kararrakin zabe.
Da yake rokon a kwantar da hankula tare da hana duk wani abu da zai kawo cikas ga zaman lafiya, Rarara ya bukaci jama’a da su marawa kokarin ‘yan sandan Najeriya da sauran jami’an tsaro baya.
Yayin da hukuncin kotun koli ke gabatowa, Mawakin na karfafa gwiwar al'umma da su rungumi zaman lafiya, tare da karfafa amanna cewa zaman lafiya shi ne babban ginshikin ci gaba da cigaba, da haɓaka yanayin jituwa da lumana, ba tare da la’akari da bambancin siyasa ba.