Gwamnatin jihar Kano ta musanta duk wasu rahotanni da ake yadawa cewa an tsawaita lokutan komawa makaranta ga dalibai
Wata sanarwa da daraktan wayar da kan al'umma Aliyu Yusuf ya fitar tace, an jawo hankalin ma’aikatar ilimi ta jihar Kano kan wata sanarwa da aka yada cewa an tsawaita ranakun komawa makarantu daga hutun zango na 3 da mako guda.
Masu yada wannan jita-jita waɗanda a koyaushe suke son haifar da ruɗani a cikin zukatan iyaye duk lokacin da hutu yazo ƙarewa.
Saboda haka ma'aikatar ilimi ke jan hankalin iyaye da masu kula da yara da daliban makarantun gwamnati da masu zaman kansu a jihar Kano cewa za a koma makarantun kwana ranar Lahadi 11 ga watan Satumba yayin da na ranar 12 ga watan na Satumba 2022.
Haka kuma sanarwa da Aliyu Yusuf ya fitar, ta ce, yayin da take gode wa iyaye da masu kula da yara bisa goyon baya da hadin kai, ma’aikatar ta bukace su da su tabbatar da yin biyayya ga ranar komawa makarantu saboda akwai hukunci dake jiran wadanda suka gaza bin umarnin komawa.