Al'ummar garin Kara dake karamar hukumar Gwarzo su shafe lokaci mai tsaho ba tare da samun ruwan famfo daga hukumar samar da ruwa ta jihar Kano ba.
Mutanen kauyen sun shafe sama da shekara 15 ba tare da ganin digon ruwan famfo ba.
Wannan mummunan yanayi ya sanya mazauna garin ke yin tattaki mai nisan kilomita 21 daga karamar hukumar Gwarzo zuwa karamar hukumar Karaye domin samun tsaftataccen ruwan sha.
Sun dauki tsawon shekaru suna haka, kafin daga bisani kungiyar cigaban Matasan garin na Kara suka kai daukin gaggawa ta hanyar tona rijiyoyin burtsatse guda shida a wasu muhimman wurare na garin.
Wannan abun yabawa da Matasan sukayi shine jigon rahotanmu na musamman a wannan mako da wakilinmu Kamaludeen Muhammed ya hada mana, tare da hadin gwiwar kungiyar Nigeria Health Watch.