Ra’ayoyin jahohin kasar sun rabu zuwa gida biyu kan yarjejeniyar da Gwamnatin Tarayya ta cimma da kungiyoyin kwadago na yin Karin naira dubu 35 ga ma’aikatan gwamnatin tarayya.
Yayin da wasu daga cikin jihohin suka ce za su karawa ma’aikatansu daidai da abunda gwamnatin tarayya ta tsara, wasu kuma sun ce tuni sun fara biyan ma’aikatansu Naira 10 kafin yarjejeniyar, a saboda haka ba su da wata alaka da matakin da gwamnatin tarayya ta dauka.
A yanzu haka gwamnatin jahar Enugu da Ondo sun amince su karawa ma’aikatansu naira dubu 35 a yayin da jihohin Kwara da Adamawa suka ce sun fara biyan ma’aikatansu karin naira dubu 10.
A jihohin Kebbi da Neja, gwamnatocin sun ce nan ba da jimawa ba za su zauna da ‘yan majalisar zartarwarsu domin tantance irin albashin da za a biya ma’aikatan.