Dan takarar shugaban kasa a zaben da ya gabata karkashin jam’iyyar Labour, Peter Obi, Ya musanta rade-radin da ake yi na cewar sun tattaunawa tsakaninsu da Atiku Abubakar da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso domin su hade wuri daya, ta yadda zasu samu damar karbar mulki daga hannun jam’iyyar APC mai mulkin kasa, Inda ya bawa ‘yan jam’iyyarsa tabbacin ci gaba da kasancewa a jam’iyyarsa.
Wani rahoto da aka fitar a ranar Litinin, ya baiyana cewar mutanen ukku, Atiku Abubakar da Peter Obi da kuma Sanata Kwankwaso na tattaunawa kan yadda zasu yi Hadaka, domin ganin sun wargaza jam’iyyar APC a zaben shekarar 2027,saboda zargin cewar hukuncin da kotu zata yanke ba zai yi masu dadi ba.
To sai dai Peter Obi ya musanta rahoton a lokacin da yake jawabi yayin wani gangamin yakin neman zabe da aka shirya a jihar Edo, Gabanin zaben kananan hukumomin jihar da za’a yi, Inda ya ce wasu daga cikin abubuwan da magoya bayansa zasu rika ji, jita-jita ce kawai.
Dagan an sai yayi kira ga masu neman shugabancin kananan hukumomin jihar Edo a karkashin jam’iyyar sa ta Labour, das u tabbatar sun cika alkawuran d asuka dauka, idan suka samu nasara.