Kungiyar manyan ma’aikatan man Fetur da Iskar Gas ta Najeriya PENGASSAN ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta soke lasisin ‘yan kasuwar man da ke siyarwa a farashin da ya wuce kima.
PENGASSAN, a cikin wata sanarwa da shugabanta na kasa, Festus Osifo ya fitar, ya ce kiran da aka yi na janye lasisin, ya biyo bayan karancin man da ake fuskanta a cikin watanni shida da suka gabata.
Yace ya kamata hukumar kula da harkokin man fetur ta kasa ta gaggauta tura ma’aikatanta a wurare daban-daban domin sanya ido akan yadda ake bin ka’idar sayar da man kuma duk wanda aka samu yana sayarwa fiye da kima a kwace masa lasisi.