Wasu rahotanni na nuni da cewa Jam’iyyar APC na tattaunawa da gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers domin ya marawa jam’iyyar baya a babban zaben shekara mai zuwa.
Wike da abokansa suna takun saka da shugabancin jam’iyyar PDP tun bayan da ya rasa tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar a hannun tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar.
A ranar Talata ne gwamnan ya amince tare da nuna goyon baya ga gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas wanda ke jam’iyyar APC, matakin da ya kara dagula rikicin PDP.
Da yake tsokaci kan matakin, wani jigo a jam’iyyar APC Farouk Aliyu ya ce jam’iyyar ta riga tayi nisa a tattaunawa da Wike kuma APC ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen maraba da gwamnan zuwa cikinta domin aiki tare a zaben shekara mai zuwa ta 2023.
Sai dai, jam'iyyar PDP ta bakin shugabanta a Legas, Philip Aivoji ya kalubalanci ikirarin cewa gwamna Babajide Sanwo-Olu ya samun goyon bayan takwaran nasa na jihar Rivers, Nyesom Wike.
Hakan na zuwa ne a lokacin da Jam'iyyar PDP a jihar Legas ta ce abun damuwa ne yadda gwamna Nyesom Wike ya kira gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu na jam'iyyar APC, a matsayin mai taka rawar gani ba tare da tambayar sau nawa ya gayyaci kowa zuwa Legas domin kaddamar da aikin koda Rijiyar Burtsatse ce ba kusan shekaru hudu yana mulki a matsayin gwamna.
Sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP na jihar, Hakeem Amode, shine ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa.
A jiya ne Gwamna Wike ya kasance babban bako na musamman a wajen taron shekara-shekara na kwamitin matan jami’an jihar Legas na shekarar 2022 inda ya bayar da gudunmuwar Naira miliyan dari uku, inda ya yaba da kwazon Gwamna Sanwo-Olu a kan mulki wanda mutane da yawa ke ganin ya goyi bayan gwamna Sanwo Olu a karo na biyu kan mulki.
Ita kuwa Jam’iyyar APC a jihar Rivers ta soki tallafin da gwamna Wike ya bayar a baya-bayan nan.