Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, Ya koka game da tsadar Man Dizal, inda yace al’amarin na shafar kasuwancinsa.
Obasanjo wanda ya baiyana haka a ranar Talata, Yayin wani taron masu sana’ar kiwon Kifi na yankin Kudu maso yammacin kasar nan, Yace tsadar da man dizal da kuma kayan abincin kiwon kifi suka yi a kasar nan, zai sa masu sana’ar kiwon kifi da dama barin sana’ar, har sai dai idan sun yadda da yadda farashin abubuwan yake kasancewa.
Ya kara da cewa a yadda ake siyar da litar man dizal kan naira 800 a halin yanzu, sannan kuma Kilo 1 na kifi yana kaiwa 1400 babu wata riba da mai sana’ar kiwon kifi zai samu, har sai idan ya sayar dashi kan naira 1500 ko kuma sama da haka.