On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Obasanjo Ya Bukaci Gwamnati Ta Tallafawa Masana'antu

Obasanjo

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya baiyana bukatar dake akwai ga gwamnati kan ta karfafa gwiwar masu masana’antu da kuma kananan yan kasuwa domin dakile shigo da kayayyaki a kasar nan.

Ya baiyana haka ne a birnin Abeokutan jahar Ogun  ya yin da yake gabatar da jawabi kan rawar da  masu kananan kasuwanci ke takawa a bangaren masana’antu da kuma hana shigo da kayyaki, yayin bude wani kanfanin kera kujerun alfarma  mai suna Olatunde Pristige Chairs Limited.

Taron wanda ya samu wakilcin mai dakinsa Bola Obasanjo, Ya baiyana muhimmanci da  masana’antu ke dashi a bangaren ciyar da tattalin arzikin kasa gaba da kuma  samar  da aiyukan yi ga dimbin matasa.