kungiyar malamai ta kasa, NUT, ta yi barazanar shiga yajin aikin gama gari idan har gwamnatin jihar Kaduna ta gaza janye matakin korar malamai dubu 2 da 357 ciki har da shugabanta kungiyar na jihar Audu Amba da gwamnati tayi.
Kungiyar ta bayyana matsayar ta ne a ranar Laraba, yayin taron majalisar kolinta na kasa a gidan malamai dake Lugbe, Abuja.
Mataimakin shugaban kungiyar NUT na kasa Kelvin Okonkwo, ya ce korar ta biyo bayan kin amincewa da shugaban kungiyar malamai na jihar Kaduna da wasu malamai suka yi na rubuta jarabawar cancanta da gwamnatin jihar Kaduna ta shirya da sauran wasu batutuwa.
Kungiyar ta bayyana cewa, a maimakon gwamnatin jihar Kaduna ta dauki matakin korar, kamata ya yi ta duba hanyoyin da zata bi domin horas da Malaman domin samun kwarewa.