Kwamitin karbar mulki na jam’iyyar NNPP a jihar Kano ya fitar da jerin sunayen kananan kwamitoci 31 na bangarori daban-daban da kuma sassan tsarin mika mulki.
Shugaban kwamitin Dr Abdullahi Baffa Bichi, wanda ya bayyana sunayen kananan kwamitocin a ranar Alhamis, ya ce tsarin mika mulki zai aiki tukuru don ganin an yi nazari da kuma rubuta duk abin da aka gada daga hukumomi da ma’aikatun gwamnati yadda ya kamata.
Wata sanarwa da Sanusi Bature Dawakin Tofa, Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamna mai jiran gado ya fitar, ta lissafa kananan kwamitocin da suka hada dana Ilimi da Kiwon Lafiya da dawo da dukiyoyin Jama’a da Ayyuka da Harkokin Mata da Ci gaban Jama’a sai Gidaje da Sufuri.
Haka kuma akwai Muhalli da Yanayi da Kudi tare da Kasafin Kudi da Tsarin Tattalin Arziki da kuma Albarkatun Ruwa.
Dr Bichi ya bukaci dukkan mambobin kwamitoci daban-daban da su zage damtse wajen gudanar da ayyukansu tare da tabbatar da kwazo da cikakkiyar kwarewa wajen gudanar da ayyukan.