Shugaban kungiyar IPOP masu fafutukar neman kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu ya koma hannun hukumar tsaro ta farin kaya DSS a ranar Lahadi, kwana guda bayan an sallame shi domin duba lafiyarsa da likitansa ya yi.
Idan za'a iya tunawa a ranar 20 ga watan Yuli ne babbar kotun tarayya da ke Abuja ta umarci hukumar ta DSS da ta baiwa Kanu damar ganawa da likitocin sa, inda ta yi watsi da rashin amincewar DSS kan bukatar.
A cewar IPOB, ana zargin Kanu yana fama da ciwon kunne kuma yana bukatar tiyata.
Lauyan shugaban kungiyar ta IPOB, Ifeanyi Ejiofor, ya shaidawa manema labarai a ranar Lahadin cewa Kanu, wanda ke tsare tun 2021, ya samu damar ganawa da likitocinsa na kashin kansa, kuma an mayar da shi magarkama.