Kungiyar kwadago ta kasa ta zargi rundunar ‘yansanda ta kasa da lakadawa shugabanta na kasa Joe Ajaero duka, bayan sun yi awon gaba dashi a tsakar ranar jiya a jihar Imo.
Shugaban yada labarai da hulda da jama’a na kungiyar, Benson Upah shine ya baiyana haka ta cikin wata sanarwa da ya fitar a daren jiya, lokacin da yake tabbatar das akin shugaban nasu, bayan ya wuni a hannun jami’an yansanda.
Jami’an yansanda sunce sun tsare shugaban kungiyar kwadagon ta kasa ne domin bashi kariya bayan ya fuskanci cin zarafi.
Sai dai jim kadan da sakin shugaban kungiyar kwadagon ta kasa kwamared Joe Ajaero ya tabbatar da cewar an lakada masa duka sannan aka yi awon gaba dashi zuwa wani wuri da bai sani, wanda a nan ne aka gallaza masa.