Kugiyar Kwadago ta NLC ta musanta wasu rahotanni dake baiyana cewar, tana shirin fara yajin aiki daga yau, saboda janye tallafin mai da gwamnatin taraiyya ta yi.
A ranar larabar data gabata ce, aka tashi batare da cimma wata matsaya ba tsakanin wakilan gwamnatin taraiyya da kuma shugabannin kungiyoyin kwadago, a yayin ganawar da suka yi kan batun cire tallafin mai.
Biyo bayan wannan labari ne, wasu rahotanni suka fara yawo na cewar kungiyar ta NLC ta saka yau juma’a a matsayin ranar da zata soma yajin aiki, domin nuna bacin ranta kan janye tallafin man.
Sai dai a raddin da kungiyar ta NLC ta yi, ta hannun kakakinta Benson Upah, Ya yi kira ga ‘yan Najeriya da suyi watsi da rahotannin, inda ya ce kungiyar tasu zata cigaba da sanar da al’umma halin da ake ciki, da kuma irin matakin da zata dauka, bayan kammala ganawarta da wakilan gwamnatin taraiyya a yau.