Gamaiyyar kungiyoyin kwadago na kasa sun nuna rashin amincewar su da saka shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, a matsayin wakilin gwamnatin taraiyya da zasu tattauna dashi kan batutuwan da suka shafi rage radadin janye tallafin man fetir da gwamnatin taraiyya ta yi.
Shugaban kungiyar kwadago na kasa, Kwamared Joe Ajaero ne ya tabbatar da haka a jiya, a yayin wata ziyara da shugabancin kungiyoyin kwadago suka kai zauren majalisar dattawa.
Ya ce aiyuka sun yiwa shugaban ma’aikatan yawa, wanda hakan yasa ba lallai ya rika halartar ganawar da zasu yi ba, Ya kuma koka kan yadda aka kwashe kusan watanni biyu batare da anyi wani zama tsakaninsu da kwamitin tsara sabon albashi da shugaban kasar ya kafa ba.
Shima shugaban kungiyar kwadago ta TUC, Festus Usifo ya koka kan tafiyar hawainiya da ake samu dangane da matakan rage radadin janye tallafin man fetir da gwamnati ta yi alkawarin samarwa.
Ya ce shugabancin majalisar dattawa ya basu tabbacin cewar zai gana da shugaban kasa domin ganin an warware matsalolin ta cikin ruwan sanyi.