A halin yanzu, Ba lallai ba ne gamaiyar kungiyoyin kwadago su dauki matakin tafiya yajin aiki daga ranar 14 ga watan da muke ciki, kamar yadda suka sanar tun da farko.
Hakan ya biyo matakin da gwamnatin taraiyya ta dauka, na janye karar data kai 'yan kwadagon, bisa zarginsu da kin mutunta umarnin kotu, bayan zanga-zangar nuna adawa da tsadar rayuwa da suka yi a Larabar makon jiya.
Shugaban kungiyar kwadago na kasa, Kwamared Joe Ajaero ne ya tabbatar da matakin a daren jiya, yayin wata hira da aka yi dashi a gidan Talabijin na channels.
Idan ba a manta ba a makon jiya ne, gwamnatin taraiyya ta maka kungiyar kwadago gaban kotu, bisa zarginsu da kawo wargi ga umarnin da Kotu ta bayar tun da farko na hana su yin zanga-zanga, Wanda hakan yasa kungiyoyin baiwa gwamnatin taraiyya wa'adin kwanaki 10 data janye karar ko kuma su shiga yajin aiki.
Sai dai Shugaban kungiyar kwadago na kasa, ya tabbatar da cewar gwamnatin taraiyya ta janye karar, kamar yadda aka aike masu da wasika da tsakar ranar jiya.