Kanfanin sarrafa Albarkatun mai na kasa , yace , Ya siyarwa Kasar Portugal Gas na kimanin Dala Bilyan 1 a bana.
An baiyana haka ne yayin wani taron tatttaunawa kan harkokin kasuwanci tsakanin Najeriya da Portugal, wanda aka gudanar a wani bangare na ziyarar da shugaban Kasa Muhammadu Buhari keyi a kasar.
Shugaban kanfanin mai na kasa Mele Kyari Yace Najeriya Ta dauki tsawon lokaci tana siyarwa kasar Man Gas, kamar yadda ya baiyaan haka a shafinsa na twitter.
Kazalika Taron ya kuma tattauna kan harkokin da suka shafi Diplomasiyya da kuma harkokin ilimi tare da inganta alakar kasashen biyu.