Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun kakaba dokar hana fitar da Makamashin iskar Gas zuwa Najeriya da wasu kasashe, kamar yadda yake kunshe cikin wata sanarwa da gwamnatin ta fitar a ranar Talata 3 ga watan Oktoban da muke ciki.
A cewar sanarwar, ya kamata a yi amfani da iskar gas da ake samarwa a cikin gida domin wadata kasuwannin dake jamhuiryar Nijar.
A cikin shekarun da suka gabata, Nijar na fitar da iskar gas zuwa makwabciyarta Najeriya, kuma kasashen biyu sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna kan shigo da albarkatun man fetur a cikin shekarar 2022.
An sanya hannu kan yarjejeniyar a hukumance a gaban tsohon karamin ministan man fetur na Najeriya, Timipre Sylva da Foumakoye Gado, wanda ya wakilci jamhuriyar Nijar a lokacin.