On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Ni Na Bada Shawarar Sauya Sunan Maryam Shetty Daga Ministocin Tinubu - Ganduje

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Gnaduje ya tabbatar da cewa shine ya amince da maye gurbin tsohuwar minista da aka nada daga Kano, Maryam Shetty da tsohuwar kwamishiniyarsa, Mariya Mahmoud Bunkure.

Ya ce sunan Shetty ya fito ne daga masu baiwa shugaban kasa Bola Tinubu shawara kan zaben ministocin da ya nada ba tare da tuntubar shi ba a matsayinsa na  tsohon gwamna.

Ganduje ya kara fayyace cewa damuwa da kuma korafe-korafen da akayi akan Shetty ta kafafen sada zumunta ya sa Tinubu ya tambaye shi ko shineya bada sunan Maryam Shetty sai ya ce a’a.

A cewarsa, a lokacin da Tinubu ya tambayi ko akwai bukatar a maye gurbin matashiyar, ya amsa da cewa kwarai da gaske, domin kuwa mukamin minista na bukatar wanda yake da dattako da  ilimi da gogewa da bada gudunmawa a jam’iyya.

Ya kara da cewa, ya bada  shawarar shugaban kasa ya nada Dr Mariya Bunkure, tsohuwar kwamishiniyarsa ta ilimi mai zurfi daga Kano ta Kudu kasancewar al’ummar yankin na korafin samun karancin damarmaki a siyasa.