On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

NDLEA Ta Kama Wata Mata Da Hodar Iblis A Filin Jirgin Sama Na Mallam Aminu Kano

Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA da ke filin jirgin saman Malam Aminu Kano sun kama wata mata mai suna Bilkisu Mohammed Bello, ‘yar shekara 45 dauke da  hodar iblis a lokacin da take shirin shiga jirgi zuwa kasar Saudiyya.

Kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja, inda ya ce an kama wadda ake zargin a makon jiya ranar Talata.

A cewar sanarwar, wadda ake zargin ta amsa cewa daurin  hodar iblis da aka ba ta ta hadiye shine kafin jirgin ta ya tashi a wani gida da ke unguwar Farawa a Kano.

Babafemi ya kara da cewa a lokacin da ta jagoranci jami’an hukumar ta NDLEA zuwa gidan, an samu kunshi 52 na miyagun kwayoyi da nauyinsu ya kai gram 767.