Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta kwace kilogram Dubu 155 na miyagun kwayoyi Daban-Daban tare kuma da Cafke masu tu’ammali da kwayoyi Dubu 5,341 cikin wata Biyar a fadin kasa
Shugaban Hukumar , Birgediya janar Buba marwa mai Ritaya shine ya shaida haka yayin Taron karawa juna sani na Dakilewa tare da bayar da Horo da kula da Lafiya kan harkokin da suka shafi tu’amali da miyagun kwayoyi wanda aka shiryawa matan Gwamnoni awani bangare na Bikin Ranar yaki da miyagun kwayoyi ta Duniya da ake Gudanarwa a kowacce Ranar 26 ga watan da muke ciki ta kowacce shekara ,wanda daya Gudana a Abuja
Kazalika Marwa ya ce taron bitar na da matukar muhimmanci ga dabarun da ake bi na dakile cin zarafi da fataucin miyagun kwayoyi da kuma illar dake tattare da shan miyagun kwayoyi a kasar nan, kasancewar an bayyana Nijeriya a matsayin babbar kasa mai nomawa tare da zukar tabar wiwi.