Kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa, Ta ce ba dole ba ne Hukumar zabe ta kasa ta rika tura sakamakon zabe kai tsaye ta hanyar amfani da na’ura, Inda ta baiyana cewar Hukumar tana da ‘yancin yin amfani da hanyar da ta yi niyyar yin amfani da ita wajen tura sakamakon zabe.
Kotun ta baiyana cewar, Na’urar tantance masu zabe ta BIBAS ita ce aka wajabtawa hukumar zaben ta kasa yin amfani da ita.
Kazalika kotun ta yi watsi da zargin da Atiku Abubakar da jam’iyyar sa ta PDP suka yi na cewar, Tinubu ba cikakken dan Najeriya ba ne, kuma yana da shaidar zama ta ‘yan kasashe guda biyu.
Haka zalika kotun ta yi fatali da zargin da masu kara suka yin a cewar Tinubu bai cancanci tsayawa takarar shugaban kasa ba, saboda zarginsa da aikata lefuka a kasar Amurika.