Kwalejin fasahar sarrafa amfanin gona ta gwamnatin dake Hotoro a Jihar Kano tace nan bada jimawa ba kayyakin da take samarwa zasu fara shiga Kasuwanni domin rage asara da samar da ayyukanyi.
Da yake jawabi jim kadan bayankaddamar da wasu Injina dake sarrafa kayan gona da kammala horo ga malamai, shugaban kwalejin Dr Muhammad Yusha’u Gwaram, yace Injinan sun hadar dana sarrafa tumatir da tattasai da masara da sauran amfanin gona.
Gwaram ya kara da cewa kwalejin ta himmatu wajen yin rijista da hukumomi da suka dace domin fara sayar da Tumatur da take sarrafawa da sauran kayyaki domin samawa makarantar kudaden shiga da inganta koyo ga dalibai.
Yace bisa ga sahalewar gwamnatin tarayya an kashe milliyoyin kudi wajen sayen na’urorin a matakin rukuni-rukuni tun daga shekarar 2019.
Yace malaman kwalejin12 sun samu horo daga kwararrun masana na cibiyar bincike dake Zaria bisa jagorancin Injiniya Bincent Oriah
Amadadin wadanda suka amfana da horon, malama Hanifa Tahir da Aisha Muhammad Goni sun godewa shugaban makarantar Dr Muhammad Yusha’u Gwaram bisa Jajircewarsa wajan ciyar da kwalejin gaba.