Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana sabbin tsare-tsare da gwamnatinsa ta bijiro dasu domin dena yin amfani da kananzir a kasar nan nan da shekara ta 2030, a wani bangare na kudurin da Najeriya ta dauka na samar da yanayi mai inganci da kuma magance dumamar yanayi.
Shugaban ya bayyana hakan ne jiya a yayin wata tattaunawa da shugaban kasa Amurka Joe Biden ya jagoranta kan babban taron bunkasa tattalin arziki kan samar da makamashi da sauyin yanayi, wanda aka gabatar kai tsaye ta hanyar allon gani gaka.
Shugaba Buhari ya zaiyana irin kudaden da kasar nan ke kashewa wajen tabbatar da kudurorin, cikinsu hadda kara yawan Motocin Bas da jama’a zasu rika amfani dasu a bangaren sufuri, da bijiro da tsare-tsaren magance saran daji da kuma kona shi.