Kungiyar Masu harkokin Sufurin Jiragen Sama ta Duniya ta ce kamfanonin jiragen sama na Najeriya da sauran wadanda suke a nahiyar Afirka za su yi asarar dala miliyan 700 a shekarar bana, sakamakon yakin da ake kan yi tskaanin kasar Rasha da Ukrain da kuma annobar COVID-19.
Kungiyar ta baiyana haka ne yayin taronta shekara-shekara karo na 78 da ake yi a birnin Doha na kasar Qatar.
Kungiyar ta IATA ta ce hauhawar farashin kayayyaki,da karin kudin ruwa zai cigaba da shafar harkokin sufurin jiragen sama a duniya, tana mai jaddada cewa ya kamata kasashe su yi koyi da irin matakan da aka dauka a lokacin da ak samu barkewear annobar COVID-19.
Kazalika kungiyar tace ya zama wajibi masu ruwa da tsaki su dauki matakan da suka dace domin magance matsalolin da suke kawo katsalandan ga bangaren sufurin jiragen sama a Duniya.