Gwamnatin tarayya tace Najeriya za ta daina shigo da tataccen mai daga kasashen waje a shekarar 2023.
Shugaban Kamfanin Mai na kasa NNPC Mele Kyari, ya bayyana haka ne Fadar Shugaban Kasa a lokacin jawabin da Sashen Yada Labarai na fadar ya shirya karo na 49. Ya ce za a daina shigo da tattacen mai ne da zarar matatar mai da attajirin Afirka, Aliko Dangote ke ginawa ta fara aiki a tsakiyar 2023.
A shekarar 1957 aka fara hako man fetur a Najeriya, wanda a 1960 ta fara fitarwa zuwa kasuwanni duniya.
Amma bayan shekaru kasar ta koma amfani da kaso mai tsoka na kudaden da take samu daga danyen manta wajen sayo tattacensa daga waje domin amfani da shi a cikin gida.
Hakan kuwa ta faru ne sakomakon shekaru da aka shafe na rashin zuba jari yadda ya kamata gami da cuwa-cuwa da suka yi wa bangaren katutu.
Kyari, yace fara aikin matatar Dangone zai sa a samu karin karfin tace danyen mai a cikin gida, wanda bayyana cewa zai kawo karshen shigo da tataccen mai daga waje.
A cewarsa, zuwa tsakiyar shekarar 2023, Najeriya za ta iya wadata kanta da tataccen man da take bukata, musamman idan aka kammala gyaran matatun gwamnati da kuma matatar Dangote wadda Gwamnatin Tarayya da ke kashi 20 cikin 100 na hannun jari.
Kyari ya ce hannun jarin da NNPC ke da shi a Matatar Dangote ya ba shi karin damar kashi 20 cikin 100 na duk abin da matatar ta samu.
Ya kuma kara jaddada cewa gwamnati na yin abin da ya kamata domin farfado da matatunta da ke sassan Najeriya.