Majalisar dattawa ta karkashin kwamitinta mai sanya ido kan baitul malin gwamnati, Ya nuna rashin amincewarsa da Ministar kudi ta kasa Zainb Ahmed, dangane da Daftarin tsare-tsaren kasafin kudin kasar nan na shekarar 2023 zuwa 2025.
A yayin zaman da kwamitin ya shirya a ranar Talata, Ministar ta baiyana cewa kasafin kudin shekara mai zuwa zai kai naira tiriliyan 19 da bilyan 76, amma kuma za’a samu gibin naira tiriliyan 12 da bilyan 43 a sakamakon harajin shigo da kayayyaki wanda zai lakume naira tiriliyan shida da kuma biyan kudin tallafin mai wanda zai lashe naira 6 .
Ministar Kudi Zainab Ahmed
A sakamakon nuna bacin ran da shugaban kwamitin sanata Olamilekan Adeola yayi, a bisa haka ne ya fadawa ministar cewa ya zama wajibi a sake yin nazari kan gibin kudin da ministar ta baiyana wanda tace dole sai an ranto naira tiriliyan 12 a badi domin cikin kasafin kudin.