Najeriya ta yi hasarar damar hakowa da sayar da kusan ganga miliyan Dubu 65 da 700 ta danyen mai a cikin shekara guda da ta wuce, sakamakon matsalolin fasa bututun mai da kuma satar danyen mai.
Hakan yana nufin anyi asarar kusan Naira tiriliyan 2 da bilyan 3 na kudaden shigar mai da kasar nan ke samu.
Shugaban Kamfanonin Shell a Najeriya, Dr Osagie Okubor ne ya bayyana haka a wajen taron kolin samar da makamashi na kasa da kasa da aka kammala a Abuja.
A cewarsa, Najeriya na sarar ganga dubu 180 a kullu yaumin saboda aiyukan masu fasa bututun mai da kuma satar shi da ake yi.
Wani bincike ya nuna cewar daga watan Maris din bara zuwa yanzu kasar nan ta yi asarar ganga milyan dubu 65 da 700.